1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zaman lafiya a Dafur

April 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0W

ƙungiyar gamaiyar Afrika ta gabatar da wani sabon daftarin zaman lafiya a Dafur tare kuma da buƙatar dukkan ɓangarorin dake gaba da juna a lardin na yammacin Sudan, su gaggauta sanya hannu a kan yarjejeniyar domin ɗorewar zaman lumana da cigaban yankin. Zagayen tattaunawa da aka yi a baya har sau bakwai, ya gaza shawo kan faɗan daya ɓarke tsawon shekaru biyu a yankin na Dafur wanda ke zama ɗaya daga cikin taádi mafi muni a duniya na cin zarafin alúma. Sabon Daftarin zaman lafiyar da ƙungiyar gamaiyar Afrikan ta gabatar, ya bada masalaha ga ƙorafin da ƙungiyoyin yan tawayen Dafur suka yi, cewa gwamnatin ta Sudan, ta mayar da su saniyar ware. ƙungiyar ta yi kira ga Shugaban ƙasar Sudan Omar El-Bashir, ya sanya ƙwararen masani a kan Dafur wanda yan tawayen suka gabatar tun da farko, daga cikin manyan mashawartan sa. Manazarta na baiyana yunkuri da cewa wani gagarumin cigaba ne a ƙoƙarin da ake na samar da dauwamammen zaman lafiya a Dafur. Wannan dai shi ne karon farko a cikin ƙudiri guda da aka gabatar da shawarwari da za su zamanto waraka ga dukkanin matsalolin waɗanda suka haɗa da rabon arzikin ƙasa dana madafan iko da kuma shaánin tsaro.