1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zaɓe a Cote d'Ivoire

October 29, 2010

A yayinda a Cote d'Ivoire ake shirye-shiryen zaɓe a can Nijeriya hukumar EFCC ta nemi da a kawar da wasu 'yan siyasa 55 daga takara a zaɓe mai zuwa

https://p.dw.com/p/Pti4
Abidjan, shelkwatar kasuwancin Cote d'IvoireHoto: DW

Yau dai zamu fara ne da rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta leƙa ƙasar Cote d'Ivoire domin duba halin da ƙasar take ciki a halin yanzu bayan da a zamanin baya ta zama abar misali a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce:

"A zamanin baya al'umar Cote d'Ivoire kawai suna samun labarin tashe-tashen hankula ne ta kafofin yaɗa labarai, amma daga baya ita kanta sai ta tsunduma a cikin rikici sakamakon rarrabuwar kawunan al'umar ƙasar abin da yayi sanadin taɓarɓarewar tattalin arziƙinta baki ɗaya. A dai ranar lahadi ne aka shirya gudanar da zaɓe na farko a tsakanin shekaru goma da suka wuce a ƙasar. Kuma ga alamu har yau ba ta canza zane ba, domin kuwa shugaba Laurent Gbagbo, wanda tun misalin shekaru biyar da suka wuce wa'adin mulkinsa ya ƙare zai sake tsayawa takara. Kuma abokan karawarsa sun haɗa ne da Henry-Konan Bedie da Alassane Ouattara, waɗanda suka ƙalubalance shi a zamanin baya."

A can Nijeriya kuwa kuwa hukumar yaƙi da cin hanci dake ƙarƙashin jagorancin Farida Waziri ta buƙaci tace wasu 'yan siyasa daga takarar zaɓen ƙasar da za a yi a shekarar mai kamawa ta 2011. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

Nigeria Unabhängigkeit
Lagos, shelkwatar kasuwancin NijeriyaHoto: Katrin Gänsler

"Hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC a Nijeriya ta fito da sunayen 'yan siyasa 55 da tare da bayanin laifufukan da ake zarginsu da aikatawa a wawware, wanda kuma a saboda haka take neman ganin an tace su daga sauran masu tsayawa takarar zaɓen ƙasar nan gaba. To ko ya Allah za a amsa wannan kira nata da ta gabatar ga hukumar zaɓe. Aƙalla dai a baya-bayan nan jam'iyyar dake mulki ta PDP ta sha ba da kai bori ya hau ga buƙatun hukumar zaɓe ta Nijeriya."

Har yau dai muna tare da jaridar Die Tageszeitung, wadda ta gabatar da rahoto akan matsalar ambaliyar ruwa dake addabar yankuna da dama na yammacin Afirka, amma ba tare da duniya ta ba da la'akari da lamarin ba. Jaridar ta ƙara da cewar:

Flut Nigeria Afrika 2010
Ambaliyar ruwa a yammacin AfirkaHoto: AP

"Kimanin mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne matsalar ambaliyar ruwa ke addaba yau tsawon makonni da dama, musamman a ƙasashen Benin da Togo da Nijeriya da kuma Ghana. A baya ga haka ma a Nijeriyar ana fama da matsalar cutar kwalera. Matsalar ambaliyar dai ta fi tsamari ne a ƙasar Benin sai kuma ƙasashen Nijeriya da Nijer dake gaɓar kogin Niger. Suma ƙasashen Togo da Ghana suna fama da matsala dangane da kogin Volta, wanda yayi cikowa kuma mahukuntan Ghana shawarar tsiyaye wani ɓangare na ruwan kogin karon farko a cikin shekaru ashirin da suka wuce da kuma yi wa mazauna ƙauyukan dake gaɓar kogin gargaɗi da su tashi zuwa wasu wuraren dabam saboda kare makomar rayuwarsu."

A cikin nata nazarin jaridar Neues Deutschland ta gano ne cewar a Janhuriyar Afirka ta Tsakiya an fi samun yawan salwantar rayuka fiye da sauran sassa na Afirka. Jaridar ta ce ƙasar na fama da yawan mace-mace kusan daidai da maƙobtanta na Chadi da Sudan da Kongo dake fama da yaƙi.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu