1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zaɓe a RDC

Yahouza S.MadobiJuly 18, 2006

Ƙungiyar Gamayya Turai, ta jaddada goyan baya ga zaɓɓuɓukan Jamhuriya Demokradiyar Kongo

https://p.dw.com/p/Btz5
Hoto: picture alliance

A Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo, aski ya zo gaban goshi, a shirye-shiryen zaɓen yan majalisun dokoki, da na shugaban ƙasa, da za ayi ƙarshen watan da mu ke ciki.

Wannan zaɓɓuɓka, sune irin su na farko da ake shirya ƙasar tun bayan shekaru 46 da su ka gabata.

Don cimma gagaramar nasara, ƙungiyar gamaya turai, da Majalisar Ɗinkin Dunia, sun aika tawagogin soja, da na fara hulla, domin sa iddo, a kan yada zaɓukan za su wakana.

Jannar Christian Damay, na ƙasar France, wanda shine shugaban rundunra ƙungiyar gamayya turai ta EUFOR,ya tabatar da cewa, EU ta aika sojoji, da zumar taimakawa Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ta cimma nasara shirya wannan zaɓɓuɓka.

Kuma rundunar EUFOR, ba ta da wani ɓangare da ta ke fifitawa, a cikin bangarorin siyasa daban-daban na ƙasar.

Ranar alhamis ne da ta gabata, EU ta fara aika dakartun ta a birnin Kinshasa.

Tawagar sojojin EU, za ta zama a Kongo, a tsawan wattani 4 bayan zaɓen.

Wannan runduan ta kasu gida 3.

Kashi na farko, da ya ƙunshi dakaru 1.100, na birnin Kinshasa, sannan rukuni na 2, a birnin Librevilles na ƙasar Gabon cikin shirin ko ta kwan.

Sai kuma kashi na 3, a birnin Postdam na ƙasar Jamus.

Rundunar EUFOR, na ƙarsƙashin tutar Majalisar Ɗinkin Majalisar Dinkin Dunia.

EUFOR, tare da haɗin gwiwar rundunar MONUC, ta Majalisar Dinkin Dunia, mai dakaru dubu 17, sun lashi takobin cimma nasara shirya zaɓen Jamhuriya Demokradiyar Kongo.

A nata ɓangare ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yankin tsakiyar Afrika, wato SADC, ta shiga ayarin ƙasashe da ƙungiyoyin, da su ka yanke shawara bada tallafi ga Kongo a cikin zaɓen.

Ministar harakokin wajen Tanzania, Asha Rose Migiro ta ziyarci Kinshasa, tare da tawagar SADC, domin bitar halin da a ke ciki, a sakamakon wannan ziyara ta bayana manema labarai cewar:

To saidai, duk da matakan tsaro da a ka tanada, akwai ruɗanin ɓarkewar rikici a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ta la´akari da ƙaurcewa zaɓen da babbar jama´iyar adawa ta yi, sannan wasu daga cikin yan takara, sun ciwo tuwan fashi bayan sun z