1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

270809 LTW Bund

August 28, 2009

Zaɓuɓɓukan jihohin Saarland, Sachsen da Thüringen a ranar lahadi

https://p.dw.com/p/JKsz
Angela MerkelHoto: AP

Tarayyar Jamus dai ƙasa ce dake manyan jihohi daban-daban guda 16. A ranar lahadi mai zuwa ne za a gudanar da zaɓuɓɓukan majalisu a jihohi guda uku, kana kusan wata guda bayan nan a ranar 27 ga watan satumba mai kamawa a gudanar da zaɓen majalisar wakilai na tarayya.

Zaɓuɓɓukan majalisun dai zasu gudana ne a jihohin Saarland, Sachsen da kuma Thüringen. Kawo yanzu dai dukkannin jami'iyyun dake takara dai basa muradin haɗaka da jami'iyar masu ra'ayin kawo sauyi. Adangane da haka ne 'yan siyasa dama masu kaɗa ƙuri'u a zaɓen na ranar lahadi ke ɗokin ganin yadda sakamakon zaɓuɓɓukan zasu kasance a wannan rana.

Abunda keda muhimmanci a waɗannan zaɓuɓɓuka dai shine, suna zama tankar zakaran gwajin dafi dangane yadda na ƙasa zai kasance a watan Satumba.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dai na fatan zarcewa akan kujerar mulki a karo na biyu, bayan an gudanar da zaɓen 'yan majalisar wakilai ta Bundestag a ƙarshen watan Satumba. A yanzu haka dai ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewar Jami'iyyar haɗaka ta 'yan mazan jiya CDU/CSU ita ce ke rinjaye akan takwararsu ta SPD, wadda suka kafa gwamnatin haɗaka tare tun daga shekarata 2005 kawo yanzu.

Bisa dukkan alamu dai ana shirin kafa wata gagarumar haɗakar a jihohin Saarland Thüringen, inda a yanzu haka jami'iyar masu ra'ayin 'yan mazan jiyan ne keda rinjaye. Domin a dukkannin jihohin biyu a wannan karon zasu faɗi, wanda ke nufin suna bukatar kawance domin kafa gwamnati, anan jami'iyyar masu sassaucin ra'ayi ta SPD zata taka rawa.

Landtagswahl Hessen 2009 Guido Westerwelle
Guido WesterwelleHoto: AP

A cewar Merkel irin wannan haɗakar yana da muhimmanci a matakin tarayya musamman a yanzu da duniya take fama da matsalolin tattalin arziki.

" Merkel ta ce zan so in kafa haɗakar da zata kawo cigban ƙasa, tare da janyo mu daga durkushewa. Akan hakan nake ganin cewar jami'iyyar FPD itace mafi girma. Domin cimma manufarmu muna bukatar jamusawa su bamu dama cikin adalci"

Hakan dai shugabar gwamnatin Jamus ɗin na nufin basu damar nasarar yin rinjaye a zaɓuɓɓukan. A yanzu haka dai FDP na gudun cewar, Merkel zata bukaci haɗaka da ita, koda akwai masu rinjaye na sassaucin ra'ayi.

Tuni dai shugaban jami'iyyar FDP Guido Westeweller ya fara mafarkin wannan hadaka harma a zaɓuɓɓukan jihohin Saarland da Thüringen.

"A matsayimmu matsakaita, bawai muna bukatar karin nasara a waɗannan jihohi uku bane kawai, amma har da matakin tarayya, domin kare Jamus daga kafa gwamnatin masu ra'ayin rikau, wanda ke nufin babu gagarumar haɗaka"

Masu ra'ayin rikau dai sun kasance abokan hamayyar FDP a dukkan matakai na siyasa, wanda suma masu ra'ayin 'yan mazan jiya suka yi amana dashi. Amma halayyar masu sassaucin ra'ayi wadanda ke mulki da masu ra'ayin rikau a birnin Berlin, inda kuma nan ne katanga take ya sha banban da wannan.

Ministan harkokin wajen kuma babban Ɗan takarar jam'yyar SPD Frank-Walter Steinmeier, ya soki manufofin jami'iyyun biyu dacewar.

"Ya ce watakila hakan nada nasaba da banban-banbance ra'ayin siyasa ne. Duk da dumbin matsaloli, ana samun daidaituwar ra'ayoyi dake kawo gamayya. Sai dai bana ganin hakan zai yiwu a matakin tarayya"

Pressekonferenz Bundesaussenminister Frank-Walter Steinmeier
Frank-Walter SteinmeierHoto: AP

Yanzu haka dai Manyan 'yan siyasa a birnin Berlin na jiran yadda zata kaya a zaɓuɓɓukan jihohin Saarland da Sachsen da Thüringen. Sakamakon da zai kasance ma'aunin yadda zaɓen tarayya zai kasance nan da wata guda.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Ahmad Tijani Lawal