1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shirye shiryen zabe a Afghanistan---

Jamilu SaniOctober 4, 2004

Yan takarar shugaban kasa sun gudanar da muhawarar zabe a kasar Afghanistan----

https://p.dw.com/p/Bvfz
Hoto: AP

A yayin da ake cigaba da shirye shiryen gudanar da baban zaben shugaban kasa a kasar Afghanistan,jiya litinin biyu daga cikin yan takakar 18 da suka shiga zaben shugaban kasa suka gudanar da muhawara game da sabon zabe mai zuwa,wanda kuma aka baiyana da cewar ita irinta ta farko da yan takarar neman shugabancin kasar ta Afghanistan suka gudanar,tun bayan da yan takara suka fara gudanar da yankin su na neman zabe watan da ya gabata a kasar ta Afghanistan.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan Hamid Karzai da kuma baban mai adawa da shi a zabe tsohon ministan ilimi Yunus Qanooni basu sami halatar zauren taron da aka gudanar da muhawarar zabe ba,da cibiyar kula da kungiyoyi masu zaman kann su da aladu ta kasar ta Afghanistan ta dauki nauyin gudanar da wanan muhawara ta zabe ba.

An dai baiyana cewar rashin fitar mutane yadda ya kamata zauren da ake gudanar da muhawara baban zaben shugaban kasar Afghanistan,kwanaki kalilan kafin a gudanar da zaben tara ga wanan wata da muke ciki wata alama ce dake nuna cewar yawancin yan takara basu gudanar da yakin su na neman zabe ba.yayin da shi kansa shugaba Hamid Karzai aka ce bai gudanar da yankinsa na neman zabe ba,duk kuwa da cewar lokaci yayi nesa na kamfai din neman goyon bayan jama’a a zabe mai zuwa.

Kasa da mutane dari suka halara a zauren da aka gudanar muhawarar zabe don jin irin muhawarar da aka tafka data fi mayar da hankali kann alamuran da suka shafi matsaloli na karbar rashawa,laifukaa na yaki da kuma makomar kasar ta Afghanistan a fukar raya al’adu.

Da dama daga cikin yan takara da suka sami halartar zauren da aka gudanar da muhawarar zaben shugaban kasar Afghanistan irin su Abdul Satar Sirat da kuma Wakil Mangul,da kuma wasu sauran yan takara shida sun baiyana cewar matukar sun sami nasara a zabe mai zuwa zasu dauki matakai na gurfanar da dukanin mutanen da aka samu da aikata laifuka na yaki.

Tun kusan shekaru 25 da suka gabata kasar Afghanistan ta sha fama da matsaloli na tashe tashen hankula,wanda kuma kungiyoyin kare hakin bil adama na duniya suka zargi kungiyoyin tsagerun musulmi na kasar da laifuka na take hakokin bil adama tun lokacin ya yakin basasa ya barke a kasar ta Afghanistan a tsakanin shekara ta 1992-1996.

Shugaban kasar Afghanistan mai ci a yanzu Hamid Karzai da ake ganin shine dan takarar dake samun goyon bayan Amurka,shi ake ganin zai lashe wanan zabe.

Cikin watan Yuni na shekara ta 2002 majalisar magabata ta Afghanistan ta zabe Hamid Karzai bisa karagar mulkin Afghanistan,tun bayan da dakarun taron dangi na Amurka suka kifar da gwamnatin yan Taliban.