1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

191108 Hadsch Pilgerfahrt Deutschland

Mohammad AwalNovember 21, 2008

Aikin Hajji na ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci. A ƙarshen watan Nuwamba maniyata daga Jamus za su fara tafiya Makka.

https://p.dw.com/p/FzAI
Dubun dubatan Musulmai a masallacin Kabah dake MakkahHoto: AP

Aikin Hajji na ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci biyar wato kenan farali ne ga wanda Allah Ya ba shi iko. A kowace shekara a daidai lokacin aikin Hajji, miliyoyin Musulmai daga ko-ina cikin duniya suna zuwa Makka don sauke wannan farali. Su ma al´umar musulmai a nan Jamus ba a bar su a baya ba wajen gudanar da wannan aiki na ibada wanda a bana za su fara tashi a ƙarshen wannan wata na Nuwamba. Yanzu haka dai ana samun ƙaruwar yawan Musulmai a nan Jamus dake sha´awar sauke wannan farali. A dangane da haka shirin Taɓa ka Lashe na wannan makon ya kai ziyara a wata makaranta da ke birnin Munich inda ake bawa maniyyata darussa game da aikin Hajji. Sai a biyo a hankali domin jin ƙarin bayani a cikin shirin.

Yadda ake tarbar maniyatan ke nan a wannan makaranta. Bayan gaisuwa ta addinin Musulunci an gode musu bisa amsa wannan gaiyata domin tattaunawa akan shirye shiryen aikin Hajji.

A bisa al´ada wannan ɗakin na ba da darussan ga maniyatan, wani wurin haɗuwar ´yan makaranta ne inda ake ba su darasi na musamman. To amma a wannan karon wani kamfanin da ya ƙware wajen shirya aikin Hajji ya gaiyaci maniyatan domin ba su darussan aikin Hajji.

Wannan darasin ana yin shi ne gwari-gwari inda ta akwatin telebijin ake nunawa maniyatan ɗakin Kabah dake Makka da kuma Masallacin Annabin Mohammad SAW dake Madinah. Daga cikin maniyatan da suka halarci wannan darasin akwai maza 15 da mata biyar. Sun kuma fito ne daga ƙasashen Arewacin Afirka da Togo da Ghana da Afghanistan da kuma Iraqi. Ko da yake dukkansu sun fito ne daga ƙasashe daban-daban amma dukkansu na cike da farin ciki.

“Ina matuƙar farin ciki ganin cewa ni ma a bana ina cikin masu tafiya Hajji, domin addininmu ya wajabta mana yin aikin Hajji. Idan kana da ƙoshin lafiya da isasshen kuɗi to ya zama wajibi ke je Makka don ziyartar ɗakin Allah”

“Hajji wata tafiya ce mai muhimmanci ga kowane Musulmi. Ina murna ƙwarai da gaske da na kasance cikin maniyata a bana. Muhimmin abu a gare ni shi ne in sauke wannan farali amma ba wai don a kira ni Alhaji ba.”

Shi ma wani da ake kira Lahbabi Mounir yana farin ciki ga tafiya aikin Hajj. Lahbabi mai shekaru 33 daga ƙasar Marokko tun kimanin shekaru 10 ya shigo nan Jamus. Bayan ya kammala karatun jami´a a fannin ƙere-ƙere ya yi aure kuma bai daɗe da samun ƙaruwa ba kamar yadda ya nunar. Duk da farin cikin da yake nunawa Lahbabi Mounir na kuma nuna ɗan shakku.

“Kimanin mutane miliyan uku ke gudanar da aikin Hajji. Shi ya sa ba aiki ne mai sauƙi ba. A kullum ana fama da matsaloli kamar turereniya da dai sauransu. Saboda haka dole ne ka shirya sosai kuma ka kasance cikin natsuwa da kuma haƙuri.”

Don samun nagartaccen shirin aikin Hajji ya sa maniyatan suka hallara don samu darasi game da Hajji. Abin da suke son sani shi ne yadda Annabi Mohammad SAW ya gudanar da Hajjinsa. Suna yin tambayoyi game da abubuwan da ka iya riskansu yayin aikin Hajji da dukkan dokokin wannan farali. Wani abin da ake faɗakar da su a kai shi ne ka da su kwantanta aikin Hajji da wani yawon shaƙatawa. Domin aikin na da wahala yana buƙatar haƙuri da kuma juriya.

Tun gabanin tafiya aikin Hajji musulmai na buƙatar haƙuri ƙwarai da gaske domin suna ɗaukar lokacin mai tsawo suna tara kuɗin wannan tafiya. A bana kuɗin ƙaramar kujera ko kuma Hajji mai araha kamar yadda wasu ke kiranta a nan Jamus ta kai Euro dubu uku ban da kuɗin guzuri. Sannan babbar kujera ko Hajji ta masu hannu da shuni ko manyan mutane ta kai Euro dubu 25 wato fiye da Naira miliyan haɗu kenan. Ana yi musu masauƙi a manyan otel-otel na alatu tare da ba kowane mutum ɗaya jagora na addini.

A bana dai Lahbabi Mounir ya dakatar da tafiya hutun shekara-shekara zuwa gida Marokko, maimakon haka zai je Makkah don aikin Hajji.

“Na canza hutu na na shekara don in je Hajji. Dukkan abokan aiki na sun san da haka domin na daɗe ina shirye shiryen wannan tafiya. Sun yi min fatan alheri.”

Yanzu haka dai ana samun ƙaruwar yawan Musulmi a nan Jamus dake sha´awar sauke wannan farali, inji Adel El Rezgui wanda ke ɗaya daga cikin masu yiwa rukunin Musulman daga Jamus jagora zuwa ƙasa mai tsarki.

“Masu sha´awar zuwa Hajji suna ƙara yin yawa. Ana dai iya gane haka ta yawan maniyata da kuma kamfanonin shirya tafiya aikin Hajji. A da tsofaffi ne ke wannan tafiya, amma yanzu abubuwa sun canza. Kamar yadda aka shaidar a nan wurin ɗaukacin maniyatan matasa ne waɗanda shekarunsu ba su haura 40 ba.”

Wato kenan yanzu da akwai yawan mutane fiye da a da waɗanda ke sha´awar tafiya Hajji daga nan Jamus. To sai dai matsalar da ke akwai ita ce ba isassun kamfanonin shirya wannan tafiya. Ga wasu kamfanonin tun a farkon shekara suke kammala karɓar kuɗin kujera. Engin Karahan na gamaiyar Musulmin Görüs na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin shirya aikin Hajji a nan Jamus, ya ce a kowace shekara ana bawa ƙasar bisa dubu 20. A bana kamfanin zai yi jigilar Alhazai 2700 sannan tuni wasu maniya na Hajjin baɗi in Allah Ya kaimu, sun fara biyan kuɗin kujera.

“Muna da niyar ɗaukar ƙarin mutane amma matsalar tana gurin gwamnatin Saudiya ne wadda ke ƙaiyadewa kowace ƙasa yawan Alhazanta. A cikin shekarun bayan nan ba ta kara yawansu ba shi yasa hakan na shafan yawan Alhazai daga nan Jamus.”