1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shugaba Bush a koriya ta kudu

Zainab A MohammadNovember 17, 2005

Shugaban Amurka na cigavba da rangadinsa a Asia

https://p.dw.com/p/Bu48
Hoto: AP

A cigaba da ziyaran mako guda da yakeyi a nahiyar Asia,shugaba Geroge W Bush na Amurka a yanzu haka yana kasar koriya ta kudu ,a inda ake saran zai halarci bude taron kwararru ta fannin tattali da wasu shugabannin kasashen Pacific da Asia a gobe jumaa.

Gabannin bude taron kasashe 21 dake cikin wannan kungiya ta tattali na Asia da fasifik,shugaban na Amurka ya gana da priministan Malasia Abdullah Ahmad Badawi,inda ya bukace shi daya tursasawa Myanmar wajen inganta harkokin kare hakkin jamaa.

Directan kula da harkokin Asia na fadar gwamnatin Amurka ta white house Mike Green,yace shugaba Bush zai gabatar da wannan batu na kasar ta Myanmar a tattasunawa da zai gudanar a Burma.

Shekaru da daya da suka gabata ,Amurka ke kira ga Myanmar data rage tsanancinta way an adawa na siyasar kasar,wanda ya hadar da daurin talala da akewa sananniyar mai fafutukar kare yan dan adam din nan ,Aung San Suu Kyi.

Tun a hjiya nedai Shugaban na Amurkaka ya jaddada matsayin kasarsa akan Myanmar a wani jawabi da yayi a kasar japan.

To sai dai ayayinda ake shirin bude wannan muhimmin taro gobe a birnin Pusan,manyan jamiai na gudanar da taron sharan fage,a inda shugaba Hu jintao na kasar Sin ya bayyana alfahari dangane da bunkasar tattalin arzikin kasarsa.

An dai dauki tsauraran matakai na tsaro a Pusan,da yawan yansanda dubu 30,adai dai lokacin da ake shirin gudanar da zanga zanga na kungiyoyi daban daban ,gabannin hallaran shugabannin kasashe 21 dake kungiyar ta APEC,wanda zai dauki yini biyu yana gudana.

Baya ga wadannan yan sanda akwai kuma jamian tsaro na sirri cikin fararen kaya dake ayyukan tsaro,musamman a harabar masaukin shugaba George W Bush na Amurka.

Ana dai saran cewa kimanin mutane dubu 100 zasu gudanar da wannan gangami a gobe a birnin na Pusan dake zama cibiyar bude wannan taro na shugabannin ksashen Asia da Fasific 21.

A taron daya gudanar da manema labasru,Tong Yang dake shugabantar kungiyar wasu yan kasuwa da ake kira Hyun Jae-hyun,yace sun sha kira ga shugabannin kasashen su da ministocin kasuwanci da tattali ,akan suyi kokarin cimma yarjejeniya guda,wadda zata raya harkokin kasuwancin yankin.

ATun a jiya nedai ministocin kasuwanci na yankin na kungiyar ta APEc,sukayi kira ga shugabanninsu dasu amince da gudanar da babban taron kungiyar cinikayya ta duniya a kasar Hong Kong a wata mai zuwa ,to sai dai sun gaza wajen bayyana laifin kungiyar gamayyar turai wadda taki kara rage kudaden haraji wa kayayyakin amfanin gonad a ake shigowa dasu.

Akan wannan tsaka mai wuya da kasashen asian ke cigaba da fuskata musamman a kasuwanninsu dake da kariyxa na lokaci maui tsawo,wata manomiyar koriya ta kudu cikin bacin rai dangane da shirin sake bude kananan kasuwannin shinkafa,ta kashe kanta ,ta hanyar shanye maganin kasha kwari,saboda bakin ciki.

To sai dai a jawabin da yayi a yau a Busan shuga Hu Jintao na sin,yace babu abun razanawa a dangane da ingantuwa ta fanning tattalin arziki da kasarsa takeyi,wadda ya jaddada cewa hakan nada tasiri wajen zaman lafiya a duniya baki daya.

Shugaban na Sin dai ya isa kasar koriya ta kudun ne inda shi da shugaban Amurka,da wasu shugabanni 19,zasuyi halarci taron kungiyar tattali ta APec,inda dukanninsu zasuyi jawabi.

Gabannin bude taron na gobe ne dai,shugaba Bush ya tattauna da Shugaba Roh Moo-hyun na koriya ta kudu,inda suka cimma yarjejeniyar ,sake gudanar da tattaunawar da zata maye gurbin yarjejeniyar yaki na 1950-53,dana zaman lafiya ,tare da gargadin cewa bazaar lamunci batun makaman nuclearn koriya ta arewa ba.

Daga koriya ta kudu shugaban na Amurka zaui wuce kasar Sin ,inda zai gana da shugaba Hu Jintao,kasar daya zarga da take yancin biladama da walwalar addini.