1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHUGABA BUSH NA AMIRKA NA YI WA MASANA KIMIYYAR KASARSA KATSALANDAN A HARKOKINSU.

Yahaya Ahmed.February 23, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlk
A cikin wadanda suka sanya hannu kan takardar nuna rashin amincewa da katsalandan din da jami'an gwamnati ke yi musu wajen gudanad da ayyukansu na kimiyya, har da shahararrun masana kimiyya da suka sami lambar darajar nan ta Nobel, da shugabannin jami'o'i da kuma wasu masu fada a ji a fannonin kimiyya na Amirkan. Koke-koken da suke daukakawa game da angaza musu da fadar White House ke yi kuwa, sun hada ne da juya sakamakon binciken kimiyyar da suka gudanar, da tantance rahotannin da suka buga, da kuma rushe duk wani kwamitin da ke suka ga manufofin gwamnati. A cikin wani rahoton da masana kimiyyan suka buga, sun bayyana cewa, a tarihin Amirkan dai, ba a taba samun gwamnatin da ke yi wa masana kimiyya katsalandan a harkokinsu da kuma juya sakamakon binciken da suka gudanar kamar ta shugaba Bush ba.

Neil lane, tsohon shugaban gidauniyar kimiyya ta Amirka, na daya daga cikin masana kimiyyan da suka sanya hannu kan takardar da aka aike wa shugaba Bush. Ya bayyana cewa:-

"A duk tsawon lokacin aikina dai, ban taba ganin yadda ake ta yunkurin jujjuya ka'idojin kimiyya, da rashin bayyana sakamako, da kebe kwararrun masana daga kwamitocin ba da shawara, ko kuma rushe kwamitocin ma gaba daya, idan ba su bi ra'ayin gwamnati ba, kamar yadda ake yi yanzu."

Bisa dukkan alamu dai, kokarin da gwamnatin Bush ke yi ne, kebe duk masana kimiyya daga tsoma baki a fannonin siyasa, ko da ma wani batun na da jibinta da aikinsu. Batutuwa kamarsu dumamar yanayi, da gurbata iska, da canje-canjen yanayi da ake samu, da cututtuka kamarsu kansa, da batun makamashin nukiliya da dai sauransu na cikin fannonin da masana kimiyyan Amirka ke koke-koken cewa gwamnatin shugaba Bush na yi musu katsalandan. Kamar yadda Sherwood Rowland, wanda ya sami lambar girmamawa saboda binciken da ya gudanar kan yaduwar da'irar nan ta Ozon a sararin samaniya ya bayyanar, sakamakon da masana kimiyyar kasa da kasa suka amince da shi dangane da dumamar yanayi, an yi watsi da shi a fadar White House.

A zahiri dai, abin da gwamnatin shugaba Bush ke yi shi ne, tantance ko kuma shure duk wani sakamakon binciken kimiyyar da bai dace da manufofinta ba. Russel Train, wani tsohon masani ne a fannin kare kewayen bil'adama na Amirkan. Kuma ya dade yana shugabancin hukumar kula da kare kewayen bil'adama ta kasar, wadda ke tsara manufofin gwamnati kan batutuwan da suka shafi yanayi. Game da wannan batun ya bayyana cewa:-

"A da can lokacin da nake aiki, ba a taba zaton cewa hakan zai taba faruwa ba. Kai ko shugaba Nixon ko Ford, ba su taba yunkurin ba ni shawaraba , balantana ma a ce ga wani umarni daga fadar White House, game da yadda zan ttafiyad da aiki na ba. Amma yanzu duk kome ya canza."

A halin yanzu, an sake fiye da rabin mamabobin wani kwamitin masana kimiyya da ke binciken irin illolin da darma ke janyo wa lafiyar mutum. An sallami masanan da suka kware kan wannan aikin, sa'anan aka kawo wasu sabbin ma'aikata, wadanda ba su da wata kwarewa, wai su ci gaba da binciken. Kamar yadda Dr. Goldmann na jami'ar Hopskins ta bayyanar:-

"Jami'an gwamnatin na nuna shakku ne ga duk sakamakon binciken kimiyyar da aka gudanar, duk da sanin cewa ba su da wata masaniya game da aikin da ake yi. Suna nan ne kawai su hana duk wani matakin gyara da za a dauka."

Ita dai fadar White House tana watsi da duk wani zargin da ake yi mata a kan wannan batun. Ta sha nanata cewa, kafin ta yanke duk wasu shawarwarin da ke da muhimmanci a fagen siyasa, sai ta yi la'akari da sakamakon da binciken kimiyya ya samo. Irin wannan bayanin ne dai ta bayar game da makaman kare dangin da ta ce gwamnatin Iraki, karkashin Saddam Hussein na mallaka, amma wadanda har ila yau, ba a gano su ba. Sai dai a nan ma, ta yi watsi ne da wani rahoton da rikakkun masana kimiyyar kasar suka buga kan cewa, Iraqin ba ta da wadannan miyagun makaman da ake zarginta da mallaka. Su ma wadannan masanan sun sanya hannu kan takardar daukaka karara da aka aike wa shugaba Bush.