1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya fara ziyarar aiki a janhuriyar Czeck

June 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuJp

Shugaban Amirka GWB ya isa Prague babban birnin janhuriyar Czeck a matakin farko na rangadin kwanaki 8 a nahiyar Turai. An shirya Bush zai gana da shugaban Czeck Vaclav Klaus da FM Mirek Topolanek, wadanda dukkansu biyu ke goyon bayan shirinsa na gina kandagarkin makami mai linzami a janhuriyar ta Czeck da kuma Poland. Shirin dai ya sha suka da kakkausan lafazi daga shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ake sa rai zasu gana a kebe da Bush a lokacin taron kolin kungiyar G8 da za´a fara gobe a Heiligendamm dake nan Jamus.