1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya kare matsayin sa dangane da yakin Iraki

November 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvLV
Hoto: AP
Shugaban Amirka GWB ya yi suka da kakkausar harshe ga masu adawa da manufarsa dangane da yakin kasar Iraqi, inda ya zarge su da kokarin mayar da hannun agogo baya. Duk da zargi da korafe-korafen da ake yi cewar fadar White House ta sauya bayyanan leken asiri don samun goyon bayan kaddamar da yakin, amma Bush ya ce wannan zargi bai da tushe bare makama. A lokacin da yake jawabi a ranar tunawa da tsofaffin soja shugaban ya jaddada cewa binciken da dukkan wakilan majalisar dattijai suka yi ba gano wata shaida da tabbatar da zargin cewa gwamnatin sa ta matsawa jami´an leken asiri lamba don su ba da bayanai na boge game da shirin mallakar makaman kare dangi a Iraqi. Bush ya ce Iraqi ta zama wata cibiyar yaki da ayyukan ta´addanci.