Shugaba Bush ya wuce gona da iri game da sansanin Guantanamo
June 30, 2006Talla
An bayyana hukuncin da kotun kolin Amirka ta yanke na cewa shari´ar da kotunan soji ke yiwa mutanen da ake tsare da su a sansanin Guantanamo haramun ne, da cewa wata nasara ce ga doka. A martanin da ta mayar game da hukuncin jaridar New York Times ta yi maraba tare da cewa yana da muhimmanci a rika girmama dokokin kasa da yarjeniyoyin Geneva amma ba yadda shugaban kasa ya ke son a yi ba. A cikin hukuncin da ta yanke a jiya kotun kolin Amirka ta ce shugaba Bush ya wuce makadi da rawa a matakin da ya dauka na gurfanad da mutanen da ake tsare da su a sansanin Guantanamo a gaban kotunan soji. Kotun ta bayyana wadannan kotuna da cewa haramtattu ne a karkashin dokar Amirka da kuma yarjeniyoyin Geneva.