1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Chavez zai shiga tsakani don sakin waɗanda ake garkuwa da su a Columbia

September 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuCe

Shugabankasar Venezuela Hugo Chavez ya ce yana shirin tattaunawa da shugabannin ´yan tawayen Columbia a wani yunkuri na samun sakin wasu mutane da dama da ´yan tawayen ke garkuwa da su. Chavez ya bada wannan sanarwa ne bayan wani taro da yayi da takwaransa shugaban Columbia Alvaro Uribe a birnin Bogota. Ya ce zai gana da shugabannin ´yan tawayen a birnin Caracas amma bai fadi ranar da za´a yi wannan taro ba. shugaban na Venezuela ya je kasar Columbia ne don tattaunawa akan wata shawara wadda ke neman gwamnati ta yi musayar firsinonin ´yan tawaye da wadanda ake garkuwa da su. Wata fitattaciyar ´yar siyasar Columbia Ingrid Betancourt da wasu Amirkawa 3 na daga cikin mutanen da kungiyar ´yan tawayen FARC ke garkuwa da su.