1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Chirac ya kira wani taro game da tarzomar da ta addabi Faransa

November 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvME

Shugaban Faransa Jaques Chirac ya kira wani taron manyan ministocin sa don tattauna matakan da za´a dauka wajen kawo karshen tashe tashen hankulan da ke barazanar zama ruwan dare a fadin kasar baki daya. Taron wanda aka shirya yi yau da dare ya zo ne a lokacin da shugaba Chirac ke shan suka daga wurin ´yan adawa saboda rashin fitowa yayiwa al´umar kasar jawabi game da ringingimun wadanda suka samo asali daga unguwannin talakawa dake wajen birnin Paris. Kawo yanzu matasa da ke tarzomar sun kone motoci kimanin dubu daya da 300 tun bayan barkewar tashe-tashen hankulan a karshen makon jiya. ´Yan sanda sun ce sun kame mutane kimanin 350 daukacin su matasa ´yan asalin arewacin Afirka da kuma wasu kasashen Afirka bakar fata. Bayanw ani taron gaggawa da suka yi jiya, ministan harkokin cikin gidan Faransa Nicholas Sarkozy ya lashi takobin murkushe wannan tarzoma.