1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Erdogan ya zargi Amirka da Isra'ila

Zulaiha Abubakar
January 5, 2018

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zargi kasashen Amirka da Israila da yin kutse cikin al'amuran gudanarwar kasar Iran da ke makotaka da kasar ta Turkiyya.

https://p.dw.com/p/2qP0g
Athen Präsident Erdogan Türkei besucht Griechenland
Hoto: Getty Images/M. Bicanski

Shugaba Racep Tayyip Erdogan na sukar duk manufofin kasar Amirka ne tun bayan da shugaba Donald Trump ya sanar da amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila. Erdogan ya shaida wa manema labarai a yau yayin da yake shirin kai wata ziyarar aiki kasar Faransa cewar ba za su lamunci wasu kasashe su sa baki a harkokin cikin gida na kasashen Iran da Pakistan ba, musammam ma kasashen Amirka Isra'ila wadanda ya bayyana da cewar su ne suka haddasa rikici a kasar Irak.

Ya zuwa yanzu dai mutane 21 ne suka rasa rayukansu yayin da aka kame wasu daruruwan jama'a sakamakon zanga zangar da ta kasance kalubale ga shugabancin kasar ta Iran, tun bayan hatsaniyar da ta biyo bayan babban zabe a shekara ta 2009.