1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Faustin-Archange Touadera ya kama aiki

Abdurraheem Hassan/YBMarch 30, 2016

Shugaban ya yi alkawarin kawo hadin kai a tsakanin Musulmai da Kiristoci da ke zaman doya da manja shekara da shekaru a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1IMLB
Faustin Archange Touadera Ex-Premier Zentralafrikanische Republik
Shugaba Faustin Archange TouaderaHoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Sabon shugaban kasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera, ya yi rantsuwar kama aiki ne a ranar Laraban nan a bainar jama'ar kasar a babban filin wasan kwallo da ke babban birnin kasar Bangui.

Zentralafrikanische Republik Archange Touadera
Archange Touadera lokacin kamfeHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Shugabannin kasashe da dama ne dai suka halarci bikin bada mulkin, ciki har da shugaban kasar Guinea da na Kwango Denis Sassou Ngeusso wanda ake zaton biki ne da zai bude sabon babin tarihin siyasar kasar. Shugaban ya yi alkawarin kawo hadin kai a tsakanin Musulmai da Kiristoci da ke zaman doya da manja shekara da shekaru a kasar, tare da martaba kundin tsarin mulkin kasa ba tare da nuna banbancin akida ko addini ba. Wannan ne ma ya sa masu fashin baki akan lamuran siyasar duniya irin su Paul Melly na cibiyar nazarin siyasan duniya da ke Birtaniya, ke ganin sabon shugaban na da kwarewar da zai tabbatar da kyakkyawar fatan 'yan kasar.

To sai dai, wani batu da ke jan hankalin mazauna jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai a yanzu ga sabon shugaban shi ne, lalubo dabarun raba wasu daga cikin 'ya kasar da suka mallaki makamai da ke zama barazana ga rayuwar al'umma da dama. Christian Touaboy, na jam'iyarMovement for the Liberation of the Central African People (MLPC) na cewa akwai bukatar inganta tsaro a tsakanin al'umma.

A yanzu dai, farfado da tattalin arzikin kasar da ma batun kafa rundunar tsaro, na daga cikin abin da ke gaban sabon shugaba Touadera, to amma duk da cewa a yau kasar Faransa ta sanar da janye dakarunta da ke kasar a cewar Paul Melly na cibiyar nazarin siyasan da ke Birtaniya akwai bukatar shugaban ya hada hannu da kungiyoyin tsaro na duniya.

Zentralafrikanische Republik Blauhelmsoldat
Dakarun tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a BanguiHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo


Shi dai sabon shugaban na jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera mai shekaru 58, tsohon malamin lissafi ne, kuma tsohon shugaban jami'ar Bangui, wanda ma ya taba zama Firaministan kasar har shekara ta 2013. Ya kuma zama shugaban kasar ne bayan samun kashi 62.7 cikin dari na kuri'un zabe da aka yi watan Fabrairu wannan shekara.