Shugaba Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya
April 6, 2016Talla
Shugaban ya tsallake rijiya da baya ne sakamakon wani zama da 'yan majalisar Dokokin kasar suka yi bayan da wata kotun kasar ta kama shi da laifin take tanede-tanden kundin tsarin mulkin kasar ta yin amfani da kudaden gwamnati don gyara wani katafaren gidansa.
Tun dai a kwanakin baya ne wata hukuma a kasar ta Afrika ta Kudun ta futar da wani rahoto da ke nuni da cewar Shugaba Zuman yayi amfani da makudadan kudaden gwamnati wajen gyara gidansa da ke a yankin Kwazulu Natal, a inda gyare-gyaren suka hada da samar da katafaren wajen wanka da dakin saukar baki wanda shugaba Jacob Zuma yayi mursisi wajen kin mutunta sakamakon rahoton.