1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Kabila ya gargadi masu neman tayar da fitina

November 15, 2016

Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango ya gargadi masu neman tayar da fitina bisa jinkirta zabe da ya yi da su guji yin hakan.

https://p.dw.com/p/2SkKI
Angola | Ankunft des kongolesischen Präsidenten Joseph Kabila bei einem meeting der süd- und zentralafrikanischen Staaten in Angola
Hoto: REUTERS/K. Katombe

Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar demokaradiyar Kwango ya yi alkawarin kare 'yancin kasarsa sannan ya nemi kawo karshen tsoma baki daga kasashen ketere, yayin da ake zaman zullami sakamakon tsaikon zabe da aka samu. Shugaban ya fadi haka lokacin da ya ke jawabi ga mutanen kasar.

Wa'adin mulkin Shugaba Kabila ya na kawo karshe a watan gobe na Disamba, amma kotunan kasar sun jinkita zabe inda shugaban zai ci gaba da rike madafun iko. A watan jiya aka tabbatar da jinkirta zaben zuwa watan Afrilu na shekara ta 2018, amma babbar jam'iyyar adawa ta nuna rashin amincewa. Tun watan Satumba aka fara samun tashe-tashen hankula saboda jinkirta zaben, abin da ya janyo mutuwar mutane da dama. Shugaba Joseph Kabila ya kuma ce nan gaba kadan zai bayyana mutumin da zai gaji Firaminista Augustin Matata Ponyo wanda ya yi murabus.