1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Mubarak ya ce juyin mulki Hamas ta yi a Zirin Gaza

June 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuI6

Shugaban Masar Hosni Mubarak ya kira kwace mulki da Hamas ta yi a Zirin Gaza da cewa wani juyin mulki ne. Shugaba Mubarak ya yi kashedin cewa rikicin da Hamas ke yi da Fatah mai sassaucin ra´ayi ka iya raba kawunan al´umar Falasdinu. Lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa karo na farko tun bayan da Hamas ta karbi jan ragamar mulki a Gaza, shugaba Mubarak ya ce Masar na goyawa shugaban Fatah kuma jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas baya. Kalaman na Mubarak sun zo ne gabanin wani taron koli da zai gudana a wurin shakatawar nan na Sharm el-Sheikh inda Mubarak din zai karbi bakoncin Abbas da FM Isra´ila Ehud Olmert da Sarki Abdullah na Jordan a ranar litinin mai zuwa. A wani abin da ke zama mayar da Hamas saniyar ware Masar ta janye jakadanta daga Zirin Gaza zuwa Gabar yamma da kogin Jordan.