1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Zuma ya shiga sabon rudani a Afirka ta Kudu

Yusuf BalaMarch 31, 2016

Tuni dai bangaren adawa daga jam'iyyar Democratic Alliance, ya bayyana cewa zai fara shirye-shirye na ganin an tumbuke shugaba Zuma.

https://p.dw.com/p/1INGE
Südafrika Kapstadt Jacob Zuma Präsident
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta KuduHoto: Imago

Kotun tsarin mulki a kasar Afirka ta Kudu ta bukaci shugaba Jacob Zuma ya gaggauta biyan miliyoyin dala na kudaden al'ummar kasar da aka yi amfani da su wajen gyara katafaren gidansa.

Wannan hukunci dai na zama abin da zai kara wa shugaba Zuma tulin kalubale da ke gabansa, kama daga batun tattalin arziki da ma rauni a shugabancinsa da goyon baya da yake samu daga jam'iyyarsa ta ANC.

Tuni dai bangaren adawa daga jam'iyyar Democratic Alliance, ya bayyana cewa zai fara shirye-shirye na ganin an tumbuke shugaba Zuma daga mulkin kasar. Shugaba Zuma dai na da kwanaki 40 ya biya wadannan kudade a cewar mai shari'a Mogoeng Mogoeng kuma suma 'yan majalisa daga bangaren jam'iyyar shugaban ta ANC a cewar mai shari'a Mogoeng ba su yi abin da ya dace ba kan batun kashe wadannan kudade a kwaskwarimar gidan shugaban.