1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Ƙaasar Guinea Bisau ya gana da friministansa

April 2, 2010

shugaban ƙasar Guinea Bisau ya gana da friministansa da sojoji ke tsare da shi a gidansa

https://p.dw.com/p/MmBk
ISojojin ƙasar Guinea BisauHoto: AP

Sojoji da ke yin borai a ƙasar Guinea Bisau na ci gaba da tsare friministan ƙasar Carlos gomes junior a gidansa inda ake tsare da shi,to sai dai a yau kanfanin dilanci labarai na Faransa ya ambato cewa shugaban ƙasar na Guinea Malam Bacai Sanha ya gana da friministan nasa wanda suka yi shwarwari tare.Rahoton ya nuna cewa babban alƙali mai shigare da ƙara na ƙasar ta Guinea Amine Michel Saad shine ya zo ya ɗauƙi friministan a gidansa tare da rakiyar sojojin suka isa har a fadar shugaban ƙasar.Tun da farko dai a wani taron gaugawa da majalisar ministocin ta kira a yau ta yi allah wadai da abinda ta kira mayar da hannu a gogo baya na taka dokokin ƙasar da sojojin suka yi.

.Ko da shike haryanzu sojojin basu fito ba fili suka bayyana cewa juyin mulki ne ba sanan kuma babu wata kafar da ta bayyana haka ba, to amma masu lura da al amuran yau da gobe na hasashen yunƙurin sojojin ya saka ƙasar cikin ruɗani .

Mawallafi :Abdourahamane Hassane Edita : Abdullahi Tanko Bala