1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban ƙasar Haiti ya sanar da cewa za a gudanar da zaɓuɓukan gama gari

July 1, 2010

Gwamnatin ƙasar Haiti ta ce za'a kashe kuɗaɗe kimani miliyan 29 na dala Amurka domin shirya zaɓuɓukan shugaban ƙasa da na ' yan majalisa a ƙasar Haiti

https://p.dw.com/p/O7X5
Shugaban ƙasar Haiti Rene PrevalHoto: AP

  Shugaban ƙasar Haiti Rene Preval ya bada sanarwa cewa za a gudanar da zaɓubukan gama gari a cikin watan November mai zuwa, bayan girgiza ƙasar da ta auku a ƙasar a cikin watannin da suka gabata wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu ɗari biyu da hamsin .

Zaben wanda ya haɗa da na shugaban ƙasa dakuma na yan majalisu,shugaban hukumar wucin gadi dake kula da shirya zaɓen Pierre Louis Opont ya shedda cewa za a kashe kuɗaɗe har miliyan 29 na dala Amurka.A yanzu dai gwamnatin ƙasar Haiti ta zuba milyan bakwai na dala Amurka sauran cikon kuɗaɗen kuwa zasu zone daga ƙasashen duniya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        :  Umar Aliyu