1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban ƙasar Venezuela ya garagɗi Amirka da ka da ta kuskura ta kai wa Iran hari.

May 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuyP

A wata sabuwa kuma, shugaban ƙasar Venezuela, Hugo Chavez, wanda a halin yanzu ya ke kai ziyara a birnin London, ya gargaɗi Amirka da ta guji shirye-shiryen kai wa Iran hari. Da yake jawabi a wani taron da mai karɓar baƙwancinsa, magajin garin birnin London Ken Livingstone ya shirya, shugaba Chavez ya ce idan Amirka ta afka wa Iran saboda rikicin da ake yi da ita yanzu kan batun makamashin nukiliyanta, ƙasar za ta dakatad da haƙon man fetur, abin da zai janyo hauhawar farashin man zuwa dola 100 ko wace ganga. Idan ko hakan ya wakana, mutanen ingila da dama ne za su daina amfani da motocinsu. Bugu da ƙari kuma, Iran ta yi barazanar kai wa Isra’ila hari. Shugaban na Venezuela, ya ƙarfafa cewa, shakka babu, Iran na da hanyoyin ɗaukar wannan matakin. Sabili da haka ne ya yi wa Amiraka kashedi na ka da ta kuskura ta afka wa Iran ɗin, saboda yin hakan inji shi, zai janyo wani sakamako wanda zai fi na Iraqi muni.

Hugo Chavez na kai ziyara a birnin London ne, bisa gayyatar da magajin birnin Ken Livingstone ya yi masa. Zai kuma gana da wakilan jam’iyyun gurguzu na ƙasar. Sai dai ba a tanadi ganawarsa da Firamiya Tony Blair ba. Shugaba Chavez dai, ya sha yi wa Tony Blair kakkausar suka, saboda haɗin kan da yake bai wa shugaba Bush na Amirka.