1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban adawa a Uganda zai baiyana gaban kotu

December 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvFp

A yau ake sa ran babban abokin adawa na Uganda da ake tsare da shi zai baiyana gaban kotun soji da ta farar hula,inda zai fuskanci zargi na wasu laifuka biyu da suke dauke da hukuncin kisa.

Sai dai kuma lauyoyin shugaban yan adawan,Kizza Besigye sunce,ba zasu halarci kotun ba a yau,saboda cewarsu babbar kotun kasar ta bada umurni a dakatar da sauraron karar.

Besigye,wanda shine babban mai kalubalantar shugaba Yoweri Museveni a kasar,an tsare shine a ranar 14 ga watan nuwamba,ana zarginsa da laifin yiwa kasa zagon kasa da kuma fyade.