1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afirka ta Kudu yace baya ɗauke da cutar HIV

April 25, 2010

Shugaba Jacob Zuma yace baya ɗauke da cutar HIV/AIDS bayan da aka gudanar da gwajin Jinin sa sau Huɗu

https://p.dw.com/p/N60x
Shugaban afirka ta Kudu Jacob Zuma yace baya ɗauke da cutar HIV/AIDSHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana cewar ba ya ɗauke da cutar HIV mai haddasa cutar AIDS.

Shugaban ya furta hakan ne a lokacin wani taron gangami domin wayar da kan al'umar ƙasar game da illar cutar ta AIDS. Zuma ya ce sau huɗu ana auna jinin sa a wannan wata kuma dukkanninsu su tabbatar da cewar garau yake.

Ƙasar Afirka Ta Kudu ta kasance ƙasar da al'umarta suka fi kowa ɗauke da cutar a nahiyar Afirka inda take da masu ɗauke da cutar miliyan 5.7 daga cikin mutane miliyan 50 na ƙasar.

Don haka ake ganin sanarwar da shugaban yayi za ta taimaka wajen wayar da kan al'umarta na zuwa yin gwajin cutar da nufin rage yaɗuwar ta.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Muhammad Nasiru Awal