1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Trump ya ziyarci Isra'ila

Suleiman Babayo
May 22, 2017

Shugaban Donald Trump na Amirkya ya ce zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai samu ne kawai ta hanyar hada hannu da kuma aiki tare.

https://p.dw.com/p/2dOq3
Donald Trump und MelaniaTheophilos III Jerusalem
Hoto: Reuters/J.Ernst

Lokacin ziyara a birnin Kudus na Isra'ila, Shugaba Donald Trump na Amirka ya jadda bukatar samun zaman lafiya tsakanin bangarorin Yahudawa da Falasdinawa. Sannan ya zama shugaban Amirka na farko da ya kai ziya zuwa bangon yammacin birnin na Kudus.

Da yake jawabi jim kadan bayan sauka Isra'ila a ziyararsa ta farko a Shugaba Trump yac e babu wata hanya face ta aiki tare:

"Muna da wata dama da ta samu a gare mu domin samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki da kuma jama'arta, kawar da ta'addanci da samar da makoma ta wanzuwar lumana da zaman lafiya. To amma za mu iya cimma wannan mataki ne kawai idan muka hada hannu muka yi aiki tare."

Tun dai bayan da ya karbi ragamar mulki a watan janairu Trump yake da kwarin gwiwa bisa cewa za a cimma nasara inda yake kokarin taimakawa Israila da Falasdinu samun sulhun da har yanzu ya faskara.

Shugaba Trump na Amirka ya kuma tattauna da Firaminista Benjamin Netanyahu na Israila kana daga bisani ake sa ran zai gana da Shugaban Mahmud Abbas na Falasdinu.

Cikin shekarar 1967 Isra'ila ta samu nasarar wace daukacin birnin na Kudus wanda ya koma karkashin ikonta  lokacin yakin da ta gabza da sauan kasashen Larabawa makwabta.