1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Amurka yace ana bukatar karin kwararan matakai kan rikicin Iraqi

December 21, 2006
https://p.dw.com/p/BuWr

Shugaban kasar Amurka G.Bush yace rikicin kasar Iraqi yana bukatar daukar kwararan matakai tare da karin sadaukarwa cikin shekaru masu zuwa.

Bush yace yana duba yiwuwar karin sojojin Amurka zuwa Iraqin domin su taimaka kawo karshen tashe tatshen hankula a kasar.

Bush yayi wannan kalami ne wajen taron manema labarai na karshen shekara a fadar white House.

Shugaban na Amurka ya jaddada cewa,bai gamsu da yadda abubuwa ke gudana ba a kasar ya kuma baiyana cewa sojin sa kai a Iraqin suna kawo cikas ga kokarin Amurka na samun nasara a kasar.

Ana dai sa ran Bush ya sanarda sabbin dabarun kasarsa game da Iraqin a watan janairu mai zuwa.

A halinda ake ciki kuma sabon sakataren tsaro na Amurkan Robert Gates ya shiga kwana na biyu na ziyarar a kasar ta Iraqi,kawanaki biyu bayan an rantsar da shi.

Sai dai Gates ya fadawa komandojin dakarun Amurka a birnin Bagadaza cewa ba zai yanke hukunci kann karin sojin Amurka a Iraqin ba,har sai tattauna da dukkan bangarorin da abin ya shafa.