1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban EU ya yi gargadin cijewar Brexit

May 4, 2017

Shugaban kungiyar EU Donald Tusk ya yi kiran nuna hakuri da martba juna tsakanin Birtaniya da EU gabanin zaben Birtaniyar da ke tafe a watan Yuni.

https://p.dw.com/p/2cP30
Brüssel EU Gipfel Brexit Verhandlungen Tusk
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Meissner

Shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk yi kiran kwantar da hankula yayin da ake tada jijiyoyin wuya tsakanin Jami'ai a Brussel da kuma London game da shawarwarin ficewar Birtaniya daga kungiyar EU.

Shugaban kungiyar ta EU Donald Tusk yace tattaunawar za ta yi matukar wahala idan aka fara jayayya tun yanzu, yana mai cewa hakan na iya sa tattaunawar ta cije baki daya..

Yana magana ne kwana daya bayan Firaministar Birtaniya Theresa May ta zargi wasu jami'an EU da yin wasu abubuwa da gangan da za su yi tasiri a sakamakon babban zaben da Birtaniyar za ta yi a ranar 8 ga watan Juni.

Tusk ya shaidawa manema labarai bayan da ya ziyarci Firaministar Norway Erna Solberg cewa son zuciyar ya yi yawa kuma bai kamata a bari hankali ya gushe yadda lamarin zai tabarbare ba.