1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Falasdinawa ya bukaci gani a kasa

December 27, 2016

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi kira da a fitar da tsari a takarda da ke nuna yadda Isra'ila za ta tsayar da aikin gine-ginenta a yankin Yammacin Kogin Jodan.

https://p.dw.com/p/2Uv6X
Schweiz Sondersitzung UN-Menschenrechtsrat Mahmud Abbas
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Bukatar hakan dai na zuwa ne bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Isra'ila ta tsaida duk wasu gine-gine da ta ke yi a yankin.

Wannan matsaya dai da kwamitin sulhun ya cimma na zama ginshiki na abin da za a dora tattaunawa mai muhimmanci kan rikicin na Falasdinawa da 'yan Isra'ila, tattaunawar zaman lafiyar da za ta zama ta kasa da kasa da Faransa za ta jagoranta.

Abbas  ya ce ya na fatan tattaunawar da za a yi ranar 15 ga watan Janairu za ta zama sila ta kawo karshen mamaya da Isra'ila ke yi a yankin na Yammacin Kogin Jodan da Gabashin Jerusalem. A ranar Juma'a ce dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayan zama mambobi 14 na kwamitin suka amince da bukatar, yayin da Amirka ta zama 'yar ba ruwanta, abin da ya sanya Isra'ila ta maida martani mai zafi.