1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Gambiya Adama Barrow ya koma gida

January 26, 2017

Shugaba Adama Barrow na Gambiya ya bukaci dakarun hadaka su ci gaba da zama a kasar tsawon watanni shida don tabbatar da lumana a kasar.

https://p.dw.com/p/2WSGG
Gambia Wahlsieger Adama Barrow
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Barazanar sojojin na hadakar ce dai ta tursasawa tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ficewa daga Gambiya, inda a halin yanzu ya ke zaman gudun hijira a kasar Equatorial Guinea. Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Afirka ta Yammam, Mohammaed Ibn Chambas ya fada a Dakar babban birnin kasar senegal cewa, bukatar tsawaita zaman dakarun a Gambiya wani lamari ne da ake ganin zai inganta tsaron kasar da ake wasu-wasi a kansa.

A yau Alhamis ne dai sabon shugaban na Gambiyan Adama Barro ya koma zuwa kasar ta sa tun bayan rantsar da shi da aka yi a kasar Senegal, a ranar 19 ga wannan wata na Janairu da muke ciki sakamakon kememen da Yahya Jammeh ya yi tun farko.