1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Ghana Mista Kufour zai je Kenya a ƙoƙarin yin sulhu

January 6, 2008
https://p.dw.com/p/CkxK

A matsayinsa na shugaban ƙungiyar tarayyar Afirka AU, a cikin mako mai zuwa shugaban ƙasar Ghana John Kufour zai yi tattaki zuwa kasar Kenya inda zai yi ƙoƙarin yin sulhu tsakanin gwamnati da ´yan adawa. A cikin wata sanarwa da ta bayar ma´aikatar harkokin wajen Ghana a birnin Accra ta ce shugaba Kufour zai yi kokarin ganin an kawo ƙarshen tashe tashen hankula tsakanin kabilun kasar wanda ya barke bayan zargin tabka magudin zabe da ake yiwa gwamnatin shugaba Mwai Kibaki. Bayan ya gana da wakiliyar Amirka a Afirka, Jendayi Frazer, shugaba Kibaki ya ce a shirye ya ke ya kafa wata gwamnatin hadin kan kasa. To sai dai jagoran ´yan adawa Raila Odinga ya bukaci Kibaki da yayi murabus sannan a sake gudanar da zaben shugaban ƙasa.