1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamnatin Italia ya kammala ziyara aiki a ƙasar Brazil

March 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuOx

Shugaban gwamnatin Italia Romano Prodi, ya kammalla ziyara aikin da ya kai a ƙasar Brazil,inda ya gana da Shugaba Inacio Lula da Sylva, a game da hanyoyin inganta mu´amila, da cuɗe ni in cude ka tsakanin ƙasashen 2.

A taron manema labarai na haɗin gwiwa, da su ka kira, shugabanin 2, sun yi alkawarin gama ƙarfi, ta fannin yaƙi da ɗumamar yanayi, da kuma masanyar husa´o´i, wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen masu tasowa ,mussamman na Afrika.

Sannan sun yanke shawara tuntuɓar juna, a kai akai, da zumar ƙarfafa mu´amilar cinikaya tasakanin su.

A sakamakon wannan taro kampanonin haƙo man petur na ƙasashen 2, wato ENI ta Italia, da Petronas ta Brazil, sun rattaba hannu, a kann yarjeniya haɓɓaka masanyar husa´o´i, ta fannin bunƙasa man petur, tare da yin anfani da rake.