1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga Turkiyya da nuna sassauci a manufofinta kan Cyprus.

November 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bucr

Shugabar gwamnatin tarayyar Jamus, Angela Merkel, ta yi kira ga mahukuntan Turkiyya da su ba da ƙaimi wajen yi wa manufofinsu kwaskwarima, tare da nuna sassauci ga tsibirin Cyprus. Merkel ta yi wannan kiran ne bayan da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta buga wani rahoto game da Turkiyyan, inda ta ce, tana tafiyar hawainiya wajen yi wa kafofin siyasarta kwaskwarima. Ƙungiyar ta ce tun da aka fara tattauna batun shigar Turkiyya a sahun ƙasashen EUn a shekara ɗaya da ta wuce dai, ba a sami wani ci gaba ba, a sauyin da ake bukatar ƙasar ta yi kafin ta cika ƙa’idojin zamowa mambarta. Sabili da haka ne ta yi barazanar ba da shawarar dakatad tattaunawar da ake yi da Turkiyyan, idan mahukuntan birnin Ankara, ba su ɗau matakan hana azabtad da fursunoni ba, da kare ’yancin faɗar albarkacin bakin mutum da kowa ke da shi ba, sa’annan kuma idan ba ta sassauta manufofinta kan tsibirin Cyprus kafin tsakiyar watan Disamba ba.