1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Hisbollah Nasrallah ya nuna goyon baya ga kudurin kwamitin sulhu

August 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bumu
Shugaban Hisbollah Sayyed Hasan Nasrallah ya ce mayakan sa zasu yi aiki da kudurin MDD wanda ya yi kira a kawo karshen fadan da ake yi Isra´ila da Hisbollah. To sai dai Nasrallah ya ce ba zai yiwu a daina fadan ba har sai an amince da wata yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ita ma Isra´ila zata yi aiki da ita. Shi kuwa a nasa bangaren FM Libanon Fuad Siniora ya ce kudurin mai fa´ida ne ga kasarsa. Shugabanni a ko-ina cikin duniya sun yi maraba da kudurin na kwamitin sulhu mai lamba 1701, da nufin kawo karshen yakin tsakanin Isra´ila da ´yan Hisbollah. SGJ Angela Merkel ta yi kira da a aiwatar da ka´idojin kudurin. FM Isra´ila Ehud Olmert yace za´a tsagaita wuta a ranar litinin mai zuwa. Shi kuwa shugaban Amirka GWB ya ce manufar kudurin shi ne kawo karshen fadan nan-take.