1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta bukaci Turai kan tsari mai kyau ga 'yan gudun hijrah

Kamaluddeen SaniSeptember 14, 2015

Zeid Ra'ad Al Hussein ya bukaci nahiyar Turai da sauran kasashen duniya da su samar da nagartaccen tsari kan tafiyar da matsalolin 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1GWHl
Schweiz 30. Sitzung des UN-Menschenrechtsrates
Zeid Al -HusseinHoto: picture-alliance/dpa/S. Di Nolfi

A yayin bude taron hukumar karo na 30 a birnin Geneva Shugaban hukumar kare hakkokin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein ya jaddada kudirin hukumar na ganin mahukuntan Afirka da Amirka da yankin Asiya gami da nahiyar Turai daukar kwararan matakai masu inganci domin jin dadin 'yan gudun hijira a duniya.

Kazalika Zeid Ra'ad ya kuma jinjina wa masu zanga-zangar nuna goyan bayan 'yan gudun hijira daga sassan kasashen Tarayyar Turai a bisa yadda suka yi tsayin daka kan halin da 'yan gudun hijirar suka shiga.

Fiye dai da mutane dubu 430,000 'yan gudun hijira da suka ketara zuwa kasashen Turai a wannan shekarar wanda mafi yawancinsu sun fito daga kasashen Larabawa da kuma Afirka.