1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban hukumar Palestinawa ya bukaci Hamas ta hallita kasar Israela, ta kuma kwance damara yaki

February 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9n

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, tare da hadin gwiwar kasar Masar, sun matsa lamba ga yan kungiyar Hamas, da su amince da kasar Israela ,su kuma kwance damara yaki domin komawa tebrin shawara, wace itace hanya daya mafi tasiri, da za a iya shawo kan riginginmun, da ke gudana a yankin gabas ta tsakiya.

Musa Abu Murzuk, daya daga shugabanin kungiyar Hamas, da ke gudun huijira a kasar Syria, ya ambata yiwuwar tantanawa da kasashen dunia, da nufin share fage ga komawa tebrin shawara da Isarela , saidai ya gitta sharradin kin amincewa da duk wata barazana, da roman baka, daga kasashen na ketare, da a cewar sa, su ka kafawa Hamas kafan zuka, tun bayan nasara da ta samu a zaben yan majalisun dokokin Palestinu.

Gobe idan Allah ya kai mu ,shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, zai gana da tawagar Hamas a zirin Gaza.

Zai anfani da wannan dama, domin kara jaddada bukatar watsi da kai hare haren ta´adanci, da amincewa da kasar Isaela, sannan da zaman sulhu tsakanin bangarorin 2.