1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran ya yiwa ´yan Nijeriya ta´aziyar

May 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuyZ
Shugaba Mahmud Ahmedi Nijad na Iran ya aike da ta´aziyar sa ga wadanda fashewar bututun mai a tarayyar Nijeriya ta rutsa da su. Ina mika ta´aziyata ga shugaba da gwamnati da kuma al´umar Nijeriya bisa fashewar bututun man wanda ya halaka daruruwan mutane a wannan kasa, inji shugaban na Iran a jawabin sa na bude taron kungiyar kasashe masu tasowa ta D-8 a birnin Bali. Nijeriya tana cikin wannan kungiya kuma shugabanta Olusegun Obasanjo yana halartar taron. Wannan hadari wanda ya auku jiya a kusa da kauyen Ilado mai tazarar kilomita 45 gabas da birnin Legas, lokacin mazauna yankin ke satar mai daga bututun, yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 200.