1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran yayi Allah wadai da kalaman Mr Bush

September 6, 2006
https://p.dw.com/p/BukY

Shugaba Ahmadinajad na Iran ya bukaci kasashen yamma dasu koma turbar Allah, ko kuma in sun ki suyi nadama.

Ahmadinajad, wanda ya fadi hakan a yayin taron manema labarai, ya jaddada cewa kasar sa babu wani barazna da take ga duniya, sabanin ra´ayin hakan daga shugaba Bush .

Wani jami´in kasar ta Iran, ya rawaito cewa Jawabin na Ahmadinajad, jawabi ne dake adawa da bayanan shugaba Bush na jiya, inda yake la´antar gwamnatin kasar, da cewa ta yan kama karya ce dake kokarin mallakar makamin Atom, don yin barazana ga Amurka.

A cewar shugaba Ahmadinajad, Iran ba zata ja da baya ba a game da anniyar ta na mallakar makamin Atom, don inganta rayuwar yan kasar ba.

Bugu da kari shugaban na Iran ya kara daukaka kira ga Shugaban na Amurka, daya yarda suyi tattaunawar keke da keke ta kafafen yada labarai, don warware matsalolin dake tsakanin su.

Idan an tuna, a cikin bayanan nasa, Shugaba Bush yaci alwashin kakkabe duk wata barazana ta yan ta´adda ciki har da madugun kungiyyar Alqeda, wato Usama Bin laden.