1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus Köhler ya kalubalanci manufar EU game da Afirka

January 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuUX

A ziyarar da yake ci-gaba da kaiwa kasar Ghana shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler yayi kira da a samar da abin da ya kira dangantaka ta hakika tsakanin nahiyoyin Turai da Afirka. A lokacin da yake jawabi a gaban wani taro karo na biyu na wani zauren tattaunawa da Afirka da ya kirkiro, shugaba Köhler ya ce sassan biyu ka iya yin koyi da juna a batutuwa da dama. A yau aka bude taron na yini biyu a birnin Accra na kasar Ghana. A lokaci daya kuma shugaban ya yi suka ga manufofin tattalin arzikin KTT game da Afirka. Ya ce kungiyar EU ba zata a iya a hannu daya tana kafa shingen ciniki sannan a daya hannun tana cike kasuwannin Afirka da kayakin ta musamman na abinci. Ya ce hakan na kawowa Afirka cikas a kokarin ta na samarwa kanta kayan abinci da take bukata. Köhler ya yi kira ga kasashen Afirka da su girmama hakkin dan Adam.