1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus ya yi kira ga Amirka da Rasha

Salissou Boukari
April 15, 2018

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira ga shugaban Amirka Donald Trump da na Rasha Vladimir Putine, da su kusanci juna domin bada damar samun mafita a rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/2w4oF
Libanon Bundespräsident Frank-Walter Steinmeier in Beirut
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Malla

Shugaban na Jamus ya yi wadannan kalamai ne yayin wata hira da aka yi da shi ta jaridar Bild am Sonntag ta kasar ta Jamus. Shugaba Steinmeier wanda yake tsohon shugaban diflomasiyyar kasar ta Jamus ne,  ya ce: "Putin da Trump ne ke da alhakin bada damar kawo karshen rikin kasar ta Siriya, kuma babu wani ci gaba da za a samu mai dorewa a Siriya muddin shugabannin biyu ba su hadu wuri daya ba suka dauki mataki na kawo karshen rikicin ta hanyar tattaunawa ba."

Shugaban na Jamus ya kara da cewa, lalle ne komai baya yuyuwa a wannan rikici sai da kasashe makwabtan Siriya, amma yana da babban mahimmanci shugaban Amirka da na Rasha su dubi juna domin kawo karshen wannan rikicin gabaki dayansa. Shugaban na Jamus ya kuma ya ce ya dole ne su nuna damuwarsu kan yadda ake nuna kyamar juna tsakanin Rasha da kasashen Yamma wanda hakan ke kara daukan wani salo.