1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kanfanin Samsung na gidan yari

February 17, 2017

Kotun Koriya ta Kudu ta tasa keyar shugaban kanfanin Samsung da ke kera salula Lee Jae-yong gidan yari bisa zargin bada cin hanci ga gwamnati don neman alfarma.

https://p.dw.com/p/2Xjmf
Samsung Vize Vorsitzender Jay Y Lee (auch Lee Jae-Yong) Befragung zu Bestechungsvorwürfen
Hoto: Getty Images/Chung Sung-Jun

Matakin kotun dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da take tsaka da bincike kan badakalar cin hanci da ya yi awon gaba da kujerar mulkin shugabar kasar Park Geung-Hye. Ana zargin shugaban kanfanin da ke kera wayar salula da bada cin hancin miliyan 40 na dalar Amirka ga kawar shugabar Koriya ta Kudu domin samun alfarma daga gwamnati.

Wannan badakalar ta shafa wa kanfanin na Samsung kashin kaji, inda tuni farashin hannayen jarinsa suka fara faduwa a kasuwannin hada-hada na duniya. Shi da Lee Jae-Yong ya sha gurfana a gaban kuliya kafin daga bisani kotun ta yanke hukuncin turashi gidan kaso.

Wannan mataki dai ya zo ne kwanaki kalilan kafin kotun koli ta yanke hukunci kan sahihanci tsige shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geung-Hye koko a'a. Idan aka sameta da laifin cin hanci da karbar rashawa, kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi shirya zabe cikin kwanaki 60 masu zuwa.