1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nemen shugabancin kasar Jamus

November 14, 2016

Jam'iyyar CDU ta shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwararta ta CSU sun bayyana goyon baya ga ministan harkokin waje kana jigo a jam'iyyar SPD Frank-Walter Steinmeier don maye shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2Shco
Deutschland Steinmeier wird neuer Bundespräsident
Hoto: picture-alliance/dpa/M: Gambarini

Manyan 'yan siyasar Jamus ciki kuwa har da shugabar gwanati Angela Merkel suka amince da batun cicciba ministan harkokin wajen kasar Frank-Walter Steinmeier domin zamantowa shugaban kasa a watan Maris din da ke tafe bayan shugaba mai ci Joachim Gauk ya bar gadon mulki. Merkel ta ce ko shakka babu Steinmeier mutum ne da ya dace da wannan mukami duba da irin dattaku da kuma kwarewar da ya ke da ita. Shugabar ta gwamnati ta ce hawansa kujerar shugabancin kasa abu ne da zai taimaka wajen daidaita lamura a wannan yanayi da duniya ke ciki na halin kila-wakala.

Ita ma dai jam'iyyar CSU wadda Horst Seehofer ke jagoranta, cikakken goyon bayanta ta bada kan wannan matsayi da ake son Steinmeier ya hau inda Mr. Seehofer ke cewar amincewa da tsarin abu ne mai muhimmancin gaske kuma sun yi shi da abokan kawancesu na siyasa:

Deutschland Bundeskanzlerin Angela Merkel & Außenminister Frank-Walter Steinmeier
Shugabar Gwamnatin Jamus ta ce Steinmeier mutum ne da za ta marawa baya don zama shugaban kasa duba da irin kwarewar da ya ke da itaHoto: Reuters/A. Schmidt

"Jam'iyyun CDU da CSU sun amince kan wannan batu domin abu ne mai muhimmanci garemu. Kan wakilanmu na hade waje guda wanda hakan ke nuni da irin aminci da ma kasancewa tsintsiya madaurinki daya da muke tare da jam'iyyar CDU."

Shi ma dai Sigma Gabriel da ke zaman mataimakin shugabar gwamnati maraba ya yi da wannan cigaba da ya ce an samu, inda ya ke cewar ba wani abu ya sanya aka raja'a kan Mr. Steinmeier wajen samun wannan matsayi ba illa kwarewar da ya ke da ita musamman ma wadda ya nuna iya shekarun da ya yi ya na ministan harkokin wajen Jamus:

Joachim Gauck und Frank-Walter Steinmeier
A farkon shekara mai kamawa ce Joachim Gauk zai sauka daga shugabancin kasa wanda ake sa ran Steinmeier zai maye gurbinsaHoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

"Ministanmu na harkokin waje wato Frank-Walter Steinmeier mutum ne da ya ake gani da kima kuma musamman tsakanin al'ummar Jamus, haka ma abin ya ke a sauran sassan duniya a 'yan shekarun da suka gabata, inda ya nuna cewar kasarmu shirye ta ke ta tabbatar da zaman lafiya da ingantaccen tsaro a Turai. Wannan ya sanya da dama na son ya kasance shugaban kasarmu na gaba."

Ba ma ga ga nahiyar Turai ba, Afirka ma wata nahiya ce da ke jinjina wa Steinmeier duba da yadda ma'aikatarsa ta harkokin wajen ta tsaya tsayin daka wajen ganin lamura sun inganta yadda ya kamata. A iya lokacin da ya shafe ya na ministan harkokin waje, ya ziyarci nahiyar a lokuta daban-daban kan battutuwa da suka shafi Afirka da Turai. Guda daga cikin kasashen da suka shaida hakan kuwa ita ce Tarayyar Najeriya inda ya ziyarta akalla sau uku don karfafa dangantakar da ke akwai tsakanin kasashen biyu da kuma taimakon kasar wajen fita daga kangin da ta fada na kalubalen tsaro.