1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shugaban kasar Iraqi yace ya fara tattaunawa da kungiyoyin yan tawaye na Iraqi

April 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bv07

Shugaban kasar Iraqi Jalal Talabani yace ya kusa cimma yarjejeniya da wasu kungiyoyin sojin sa kai guda 7,wanda hakan zai iya kawo karshen tashe tashen hankula a kasar.

Yace Amurka ta fara tattaunawa da wadannan kungiyoyi tare da amincewarsa,kuma akwai yiwuwar cimma yarjejeniya.

Yace kungiyoyin suna adawa da mamayar da Amurka tayiwa Iraqi,saboda haka zaa tattauna dasu kuma zasu iya shiga harkokin siyasa na kasar.

Shugaban na Iraqi ya kuma zargi kasar Syria makwabciya,da laifin barin sojin haya shiga kasar ta Iraqi.