1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Jamus A Habasha

December 14, 2004

A ci gaba da ziyararsa ga kasashen Afurka shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya isa Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda ya gana da P/M Meles Zenawi

https://p.dw.com/p/BveD

A lokacin da take bayani Kerstin Müller cewa ta yi Jamus ta tsayar da shawarar yafe wa Habasha bashin Euro miliyan 67 da take binta ne domin rufa wa kasar baya a manufofinta na garambawul. Muhimmin abin da ake fatan gani shi ne a yi amfani da wadannan kudade a matakan yaki da matsalar talauci, musamman ta bunkasa ayyukan harkar ilimi da ayyukan noma. Manufar yafe basusukan tana da nasaba da wata daidaituwar da aka cimma a tsakanin kasashen dake ba da lamuni na gamayyar Paris Klob a game da yafe wa kasar Habasha kashi 90% na basusukan da kasashen suka tsaya mata ta karba domin tafiyar da cinikinta na ketare. A lokacin da ya kai ziyara kasar Habasha watan janairun da ya wuce shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya bayyana shirinsa na yafe wa kasar kashi dari bisa dari na basussukan dake kanta. Tun dai abin da ya kama daga shekarar 1993 kawo yanzun Jamus ta yafe wa Habasha bashin da ya kai na Euro miliyan 197. Babban abin da ake fatan gani daga Habashan, kamar yadda aka ji daga bakin karamar minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus Kerstin Müller shi ne bin nagartattun manufofi na demokradiyya da girmama hakkin dan-Adam. A makon da ya gabata al’amura sun dada yin tsamari a rikicin iyaka dake tsakanin Habasha da Eritriya. Ita dai Habasha ta ki amincewa da layin da wata hukuma ta kasa da kasa ta tsara domin fayyace zirin iyaka tsakaninta da makobciyarta Eritriya, kuma shawarar da fadar mulki ta Addis Ababa ta bayar a makon da ya wuce ba zata taimaka a shawo kan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa ba. A ganawar da suka yi da P/M Meles Zenawi, shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya bayyana damuwarsa game da halin da ake ciki inda yake cewar:

Na kawo wannan ziyarar ce domin in kara tabbatar da goyan bayan Jamus ga fafutukar cimma zaman lafiya a cikin ruwan sanyi. Domin kuwa a duk inda ake fama da rikici, walau na yanki ne ko tsakanin kasa da kasa, kamar yadda ake gani a sassa dabam-dabam na Afurka ko a tsakanin Habasha da Eritriya, ba za a samu wani nagartaccen ci gaban tattalin arzikin da zai haifar da walwala ga makomar rayuwar jama’a ba. A saboda haka wajibi ne a ba wa zaman lafiya fifiko domin samun nasarar yaki da matsalar talauci.

Shugaban na kasar Jamus dai ya yaba da irin ci gaban da Habasha ta samu akan hanyar tabbatar da mulkin demokradiyya da kuma kyakkyawar dangantaka ta kut da kut dake tsakaninta da Jamus. Horst Köhler ya gabatar da bikin bude sabon ginin cibiyar al’adun Jamus ta Goethe a Addis Abeba, kuma a gobe laraba idan Allah Ya kai mu zai kammala ziyararsa ga Habashan tare da wani jawabin da zai gabatar a zauren mashawartar kungiyar tarayyar Afurka ta AU.