1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kasar Jamus Ya Kammala Ziyararsa A Afurka

December 16, 2004

A yau alhamis ne shugaban kasar Jamus Horst Köhler yake kammala ziyararsa ta kwanaki goma ga kasashen Afurka tare da ya da zango a kasar Jibuti

https://p.dw.com/p/Bve9

Bisa ga ra’ayin shugaban kasar Jamus Horst Köhler, ita gaskiya wajibi ne a fadeta kome dacinta, kuma a sakamakon haka shugaban bai yi wata-wata ba wajen tsage wa shugabannin Afurka gaskiya yana mai fatali da manufofin diplomasiyya, inda a ganawarsa da shugaba Kerekou na Benin, yayi masa tsokaci da karatowar ranar yaki da cin-hanci ta duniya kuma ita kanta kasar Benin har yau tana da sauran rina a kaba a fafutukar murkushe cin rashawa tsakanin mahukuntanta. A duk inda ya sa kafa, Köhler ba ya rufa-rufa wajen kalubalantar abubuwan da yake gani suna hana ruwa gudu ga ci gaban al’amuran nahiyar Afurka. Ya ce lokaci yayi da kasashen Afurka zasu rika dora wa wasu kasashe na ketare alhakin rikice-rikice da yake-yakensu na basasa. Domin kuwa galibi su kansu kasashen ne ummal’aba’isin wadannan yake-yake. Kazalika ana fama da tafiyar hawainiya a matakan canje-canje ta yadda kasashen dake ba da lamuni suka fara saka ayar tambaya a game da amfanin taimakon da suke bayarwa. Afurka ba zata iya kubuta daga tserereniyar cinakayya ba kuma wajibi ne ta dauki kaddararta a hannu. Wadannan kalaman suna da muhimmanci, musamman ta la’akari da gaskiyar cewar kasashe kamar Benin da Habasha, wadanda ke kan gaba wajen samun kudaden taimako daga Jamus, galibi ba sa aiwatar da wadannan kudade a manufofin yaki da talauci, a maimakon haka kudaden na kwarara ne zuwa aljifan jami’an siyasa da sauran ukunin ‚yan gata na wadannan kasashe. To sai dai kuma kamar yadda masu iya magana su kan ce: Idan an yi ta barawo sai a yi ta mabi sau. Domin kuwa su kansu kasashen Turai ba su tsira daga kalubalen shugaban na kasar Jamus ba, inda ya sake janyo hankalinsu ga alhakin da ya rataya a wuyansu game da makomar Afurka. Ya ce wajibi ne kasashen su cika alkawarin da suka yi na bunkasa yawan kudaden taimakon raya kasa zuwa kashi 0‘7% na jumullar abubuwan da suke samarwa a shekara, nan da shekara ta 2015. A dai halin da ake ciki yanzu duka-duka abin da Jamus ke bayarwa na taimakon raya kasa bai zarce kashi 0’28 na jumullar abin da kasar ke samarwa a shekara ba. Daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu wajen ta da komadar tattalin arzikin Afurka shi ne tsauraran matakai na shingen ciniki da karya farashin kaya da kasashe masu ci gaban masana’antu ke yi, wadanda kuma Köhler ya ce wajibi ne a datakar da su. Gaba daya dai wannan ziyara ta shugaban kasa Horst Köhler tana da nufin nuna cikakken goyan baya ga canje-canjen manufofin da ake samu a kasashen Saliyo da Benin da kuma Habasha tare da janyo hankalin Jamusawa zuwa ga nahiyar Afurka.