1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Jamus ya ziyarci tashar DW

Salissou BoukariJune 10, 2016

A wannan Juma'a ce shugaban kasar Jamus Joachim Gauck cikin wani rangadi da ya yi a nan birnin Bonn ya ziyarci tashar DW, inda ya samu tarbo daga daruruwan ma'aikata.

https://p.dw.com/p/1J4bS
Bundespräsident
Hoto: DW/M.Müller

Ma'aikatan na DW dai sun fito ne da misalin karfe uku daidai agogon nan Jamus domin tarban shugaban kasar, wanda ya ce yazo ne tashar ta Deutsche Welle domin nuna goyon bayansa ga wannan tasha kan iri-irin ayyukan da take yi a fadin duniya.

Yayin wannan ziyara a nan Bonn, shugaban kasar ta Jamus Joachim Gauck, ya kuma bayyana fargabarsa kan halin tsaro yayin gudanar da wasannin cin kofin Turai da za a soma a Yammacin yau Juma'a a kasar Faransa, inda ya ce yana mai fargaban wannan gasa da ke a matsayin abun annashuwa ta fuskanci kalubale.

Ma'aikatan DW daban-daban sun yi amfani da wannan dama wajen daukan hotuna da shugaban kasar ta Jamus, wanda ya samu tarbo daga babban darecta janar na tashar ta DW Peter Limbourg da sauran manya-manyan mukarrabansa.