1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Kenya ya yi wa Gwamnati garambawul

February 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7w

Shugaban kasar Kenya Maw Kibaki, ya yi garambawul ga gwamnatin kasar.

Ya nada wasu sabin ministoci 3, domin maye gurbin ministocin da su ka yi murabus, a sakamakon tuhumar su da ake, da hannu, a cikin al´ammuran ci hanci da rashawa .

Wannan ministoci, sun yi murabus a farkon watan da mu ke ciki, domin amsa tambayoyin kotuna, a game da zargin da a ke masu, na karbar rashawa ta maggudan kudade.