1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kongo ya baiwa dakarun MDD waadin fidda magoya bayan Bemba daga Kinshasa

November 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bual

Shugaban kasar Kongo Joseph Kabila ya baiwa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya waadin saoi 48 da su fidda dakarun da suke goyon bayan abokin hamaiyarsa Jean Pierre Bemba daga babban birnin kasar Kinshasa.

Kabila wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar,yace muddin dai rundunar ta majalisar ta gagara aiwatar da wannan bujata tasa to fa zai baiwa sojin kasar suyi hakan.

Halin zaman dar dar sai karuwa yakeyi a birnin Kinshasa tun lokacinda magoya bayan Pierre Bemba suka yi wata zanga zanga a cikin kotun koli ta kasar.

Har ya zuwa yanzu kuma Jean Pierre Bemba yaki amincewa da sakamakon zaben zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 29 ga watan oktoba.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Kabila ya samu kashgi 58 bisa dari na kuriu da aka kada yayinda abokin haiayarsa Jean Pierre Bemba ya tashi da kashi kusan kashi 42.