1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kungiyar GSPC na Algeria ya gamu da ajalinsa

January 31, 2006
https://p.dw.com/p/BvA0

Kungiyar GSPC mai tsautsauran ra´ayin addinin islama, a kasar Algeria ta bayyana mutuwar shugaban ta Sheick Ahmed Abni al Bara a ciki wata arangama da dakarun gwamnati.

Sanarwar da ta bayana rasuwar Sheik Ahmed ta kara da cewa ya gamu da ajalinsa, a jihar Bedjaia da ke tazara kilomita 300 a gabancin Algers babban birnin kasar, saidai ba ta bayana ranar wannan mutuwa ba.

Kungiyar GSPC da aka kaffa a shekara ta 1998, na da alaka da Alka´ ida, ta Usama Bin Laden, kuma a halin yanzu ita ce matsayin kungiyar da ta fi tada hankullan hukumomi, a kasar Algeria.

Ta na da rassa a sassa daban daban na dunia.

Kungiyar ta yi watsi da afuwar da shugaba Abdul Aziz Buteflika na Algeria, ya ambata yi wa dakarun sa kai, na kungiyoyi

Addinin Islama, da ke tawaye da gwamnati.

Hukumomin Algeria sun kiyasza cewa a halin da ake ciki kungiyar GSPC na da a kalla dakaru dubu warwatse a cikin kasa.