1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kwalambiya ya ci lambar Nobel

October 7, 2016

Shugaba Juan Manuel Santos na kasar Kwalambiya ya lashe kyautar lambar Nobel a 2016, bisa yunkurin samar da zaman lafiya a kasarsa.

https://p.dw.com/p/2R0tG
Kolumbien Juan Manuel Santos Präsident Friedensnobelpreisträger 2016
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Vergara

Kwamitin kula da zaben wadanda suka lashe kyautar  Nobel da ke kasar Norway ya tabbatar da zaben da aka yi wa Shugaba Juan Manuel Santos na kasar Kwalambiya dan shekaru 65 da haihuwa, saboda yunkurin samar da zaman lafiya a kasar, kamar yadda shugabar kwamitin Kaci Kullmann Five ta bayyana:

"Kwamitin kula da kyautar Nobel da ke Norway ya amince da bai wa Shugaba Juan Manuel Santos na Kwalambiya kyautar ta shekara ta 2016 saboda jajircewa kan ganin an samu zaman lafiya bayan yakin basasa na fiye da shekaru 50, da ya janyo mutuwar kimanin mutane 220,000 yayin da wasu kusan milyan shida suka tsere daga matsugunansu."

Wani abu da ya fito fili shi ne an tsame shugaban kungiyar 'yan aware masu ra'ayin makisanci na FARC, Rodrigo Londono daga cikin wannan kyauta duk da cewa tare da shugaban kasar ta Kwalambiya suka sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar. Tun lokacin da Shugaba Juan Manuel Santos ya dauki madafun iko yake fafukar ganin samar da zaman lafiya, har zuwa lokaci da aka sannu hannu kan yarjejeniyar bayan tattaunawa ta tsawon lokaci a birnin Havana na kasar Kyuba.

Kolumbien Kindersoldaten FARC Armee
'Yan tawayen na FARC dai sun rika amfani da yara a matsayin sojan yakiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Dalton

Amma wani hanzari ba gudu shugaban ya gaza samun nasara kan zaben raba gardama da aka shirya saboda tabbatar da yarjejeniyar ta zaman lafiya.

Shi kansa kwamitin kula da kyautar Nobel ya ce watsi da masu zaben Kwalambiya suka yi da yarjejeniyar zaman lafiya, haka ya nuna rashin amincewa da maganar abin da aka rubuta a yarjejeniyar, ba wai 'yan kasar sun yi watsi ne da zaman lafiya baki daya ba.

Shin kansa Shugaba Santos ya ce babu gudu babu ja-da-baya kan shirin zaman lafiya a kasar ta Kwalambiya:

"Fitar da yara daga wuraren da ake yaki na zama misali na rufe wannan mummunan yanayi cikin tahirinmu kan samun zaman lafiya da sasanta juna."

Kwamitin bayar da kyautar Nobel ya nuna gamsuwa da yadda Shugaba Juan Manuel Santos ya ci gaba da shirin neman zaman lafiya duk da cikas da ya gamu da shi lokacin zaben raba gardama da 'yan Kwalambiya suka yi