1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Masar zai kawo ziyara Jamus

March 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv67

Gwamnatin kasar Jamus ta sanarda cewa nan gaba cikin wannan wata ake sa ran shugaban kasar Masar Hosni Mubarak zai kawo ziyara nan Jamus,inda zasu tattauna halin da ake ciki a yankin Palasdinawa da kuma batun demokradiya a yankin gabas ta tsakiya.

Kakakin gwamnatin Jamus,Thomas Steg,yace Mubarak zai gana da shuagabar gwamnati Angela Merkel a ranar 11 ga wata,inda ake sa ran Merkel zata nemi raayinsa game da mataki daya kamata a dauka dangane da samun nasarar Hamas a yankin Palasdinawa,zata kuma sake jaddada matsayin Jamus dangane da Hamas ta amince da kasar israila da kuma amincewa da yarjeniyoyin zaman lafiya na baya.